Talata 27 Oktoba 2026 - 19:51
Ganawar Sakataren Majalisar Tsaron Ƙasar Iran da Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci / Jaddada Bukatar Cika Sharuɗɗan Iran Domin Kawo Ƙarshen Yaƙi

Hauza/ Ayatullah Sayyid Mujtaba Husaini Khamene'i ya bayyana Majalisar Tsaron Ƙasa da sakatariyarta a matsayin “mahadar tsara manufofin ƙasa”, inda ya jaddada tasirin da fannoni huɗu na al’adu, siyasa, tattalin arziki da tsaro suke da shi a kan juna, da kuma buƙatar haɗa matakan da suka dace da kowane fanni yayin yanke shawara.

A cewar Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Manjo Janar Dakta Muhsin Riza'i, Sakataren Majalisar Tsaron Ƙasar Iran, ya gana da Ayatullah Sayyid Mujtaba Husaini Khamene'i, Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci.

Majalisar Tsaron Ƙasa ita ce mahadar tsara harkokin ƙasa

A yayin wannan ganawar, Ayatullah Sayyid Mujtaba Husaini Khamene'i ya bayyana Majalisar Tsaron Ƙasa da sakatariyarta a matsayin “mahadar tsara manufofin ƙasa”. Ya kuma jaddada yadda fannoni huɗu na al’adu, siyasa, tattalin arziki da tsaro suke tasiri ga juna, tare da buƙatar samar da tsare-tsaren da suka dace da kowane fanni yayin yanke shawara.

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci ya bayyana cewa, samun cikakken taswirar hanya da ta ƙunshi dukkan matakan aiwatar da kowane shiri, tun daga farkonsa har zuwa ƙarshensa, shi ne ginshiƙin yanke sahihan shawarwari masu ƙarfi da ɗorewa.

Daga cikin sauran batutuwan da aka tattauna a wannan ganawa akwai ƙarfafa haɗin kan ƙasa, da gina amincewa tsakanin al’umma da jami’an gwamnati. Haka kuma, an jaddada amfani da damar da Kundin Tsarin Mulkin ƙasar ya tanada, musamman Mataki na 176, domin taimaka wa shugaban ƙasa da hukumomin zartarwa wajen sauƙaƙa da kuma hanzarta magance matsalolin ƙasar.

Sauran batutuwan sun haɗa da kare tsaron ƙasa da na yankin ta hanyar gudanar da harkokin mashigar ruwa ta Hormuz, da kuma ƙarfafa dangantaka tsakanin Iran da ƙasashen maƙwabta bisa muradun da za su amfani ɓangarorin biyu cikin dogon lokaci.

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci ya bayyana cewa, yadda abokan gaba suka shiga halin rashin mafita yana daga cikin sakamakon juriyar al’ummar Iran.

Ya kuma jaddada muhimmancin sanar da al’umma bayanai cikin himma kuma a kan lokaci, domin tabbatar da ci gaba da kasancewar al’umma a fagen kare ƙasa da tsarin mulkinta.

Haka kuma, ya jaddada buƙatar ci gaba da neman tabbatar da haƙƙoƙi da muradun al'ummar Iran da kuma ƙungiyoyin Gwagwarmaya ta hanyar cika sharuɗɗan da jami’an ƙasar suka gabatar, da nufin kawo ƙarshen yaƙi da kuma yanayin da ake ciki na “ba yaƙi, ba kuma zaman lafiya.”

A yayin ganawar, Sakataren Majalisar Tsaron Ƙasa ya gabatar da rahoto kan halin da ƙasar take ciki a fannoni daban-daban, tare da bayyana ƙoƙarin da ake gudanarwa.

A cikin rahotonsa, Dakta Muhsin Riza'i ya bayyana cewa, ɗaya daga cikin matakan da sakatariyar Majalisar Tsaron Ƙasa take aiwatarwa shi ne bibiyar manufar dabarun Jamhuriyar Musulunci ta Iran na “samar da tsarin gudanarwa da tsari na yanki wanda ya samo asali daga cikin yankin kansa.”

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha